Wani ginin coci da ya rufta ya hallaka wani babban Fasto a lokacin da ya fado masa a Jihar Benue.

 

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata a Makurdi babban birnin Jihar Benue.

 

Channels TV ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a yayin da Faston da mabiyasa guda uku ke gudanar da addu’o’i a cikin cocin.

 

Rahotanni sun tabbatar da cewa sauran mutane ukun da ke tare da Faston sun tsira.

 

Ruftawar ginin ta haifarwa da wasu gidaje da wayoyin wutar lantarki matsala.

 

Bayan faruwar lamarin jami’ai a yankin sun bayar da agajin gaggawa sun fara gudanar aikin ceto a gurin.

 

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar ya bayyana cewa basu da labarin faruwar lamarin.

 

Kakakin ya ce za su gudanar da bincike akan lamarin sannan daga bisani su bayar da bayani.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: