Wasu jami’an sa-kai a Jihar Sokoto sun kai harin daukar fansa a wasu rugagen Fulani, bayan da suka hallaka mutane uku da yin garkuwa da wasu da dama a kauyen Soro da ke karamar hukumar Binji ta Jihar.

 

Wata majiya daga kauyen ta bayyana cewa ‘yan sa-kan masu tarin yawa sun isa Kauyen ne da misalin karfe 1:00am na daren ranar Litinin, tare da wasu dabbobi da ake zargin sato su suka yi daga wasu kauyuka a Jihar.

 

Shima wani mazaunin kauyen ya shaidawa Daily Trust cewa a harin farko da ake zargin Fulanin sun kai sun hallaka mutane uku suka jikkata uku, daga bisa suka yi awon gaba da wasu da dama ciki har da iyalan wani gida baki dayansu.

 

Ya ce bayan faruwar hakan ke da wuya ’yan sa-kai da ke yankin suka kai harin dukar fansa rugagen Fulani,i’ inda suka hallaka wasu maza tare da kona gidajensu.

 

Mazaunin garin ya ce sun samu wasu majiyoyi cewa Fulanin sun yi wani taro kafin harin da aka kawowa kauyen, bayan da mutanen yankin suke zargin a taron da Fulanin suka yi ne suka kawo hari yankin.

 

Kazalika ya ce dama akwai rashin jituwa a tsakanin kauyukan biyu.

 

Ya ce da dama daga cikin mutane yankin sun tsere bisa fargabar harin da aka kaiwa yankin.

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar SP Ahmad Rufa’i ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Kakakin ya ce kwamishinan ‘yan sandan Jihar Ali Kaigama ya bayar da umarnin aikewa da jami’an tsaro yankin bayan wani zama da yayi da shugabannin Kauyukan domin tabbatar da tsaro a yankunan.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: