Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa jirgin yaƙin rundunar ya samu nasarar hallaka tarin mayakan Boko Haram da ISWAP a yankin Tafkin Chadi da ke Jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar sojin samaan Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.


Kakakin ya ce jirgin yakin ya yi ruwan wuta akan maboyar ‘yan ta’addan, inda ya lalata sansanoninsu tare da makamansu.
Edward ya bayyana cewa jami’an sun kai sumamen ne a tsakanin ranakun 27 zuwa 30 ga watan Satumba da ya gabata.
Edward ya kara da cewa sun samu nasarar ne da taimakon bayanan sirri akan maboyar ‘yan ta’addan a Tumbun Fulani da Tumbun Shitu da ke yankin.
Kakakin ya ce bayan samun bayanan ‘yan ta’addan, an gano yadda zasu ƙaddamar da harin kan jami’an sojin da sauran mutanen gari.
Kazalika ya bayyana cewa a Tumbun Fulani an gano yadda ‘yan ta’adda suke zuba jarkoki a cikin manyan motoci guda biyu da aka boye a karkashin bishiyoyi.
Gabkwet ya ce bayan samun bayanan suka aike da jirgin sojin saman zuwa sansanin domin kawar da batagarin.
Edward ya ce bayan yiwa jami’an ruwan wuta aka gano da yawa daga cikin ‘yan ta’addan sun rasa rayukansu, yayin da suma motocin dakon makamannasu suka lalace.
Sannan ya bayyana cewa jami’an sun kuma kai hare-hare makamancin haka a Tumbun Shitu bayan da aka gano wasu gine-ginen da ake kyautata zaton maɓoyar ‘yan ta’adda ne a boye a cikin wani guri mai duhu.
Suma an hallaka da dama daga cikinsu.
