Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Neja ta ce zuwa yanzu an gano mutane 24 daga cikin waɗanda ibtilain kifewar jirgin ruwa ya rutsa da su.

 

A ranar Litinin ne dai aka ruwaito wani jirgin ruwa da ya taso daga jihar Kebbi ya nufi jihar Neja ya yi hatsari.

 

Jirgin mai daukar mutane hamsin kuma ya kife da mutanen.

 

Shigaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Neja Garba Salihu ya bayyana aa yau Laraba cewa, an sake gano mutane uku da lamarin ya rutsa da su.

 

Hukumar ta ce zuwa yanzu mutane Bakwai ne su ka mutu.

 

Hukumar ta ce ta na ci gaba da bincike don gano sauran mutanen da ba a gani ba.

 

A na ci gaba da fuskantar hatsarin jirgin ruwa a Najeriya wanda gwamnatin tarayya ta bayar da umarni domin bincike a kai.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: