Hukumomin Jami’ar birnin Tarayya Abuja sun bayyana cewa za su fara gwajin kwayoyi ga dukkan dalibin da ya nemi gurbin shiga makarantar.

Shugaban Jami’ar Farfesa Abdulrashid Na Allah ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a gurin shirye-shiryen bikin yaye dalibai karo na 27.


Shugban ya ce Jami’ar na son sanin halin kowanne dalibi akan kwayoyi domin taimaka musu wajen kaucewa amfani da su.
Na Allah ya bayyana cewa za su hada kai da Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa NDLEA domin taimakawa dalibai da ke ta’ammali da miyagun kwayoyi bayan kammala karatu.
Abdulrashid ya kara da cewa a yayin bikin Jami’ar za ta yaye dalibai masu digirin digirgir guda 100 sai kuma masu digiri na biyu sama da mutane 700.
Farfesan ya ce akwai wasu dalibai sama da 7,000 da za a yayesu a ranar Asabar mai zuwa, bayan kammala digirinsu a jami’ar.
Shugaban ya bayyana cewa a halin yanzu sun inganta Jami’ar ta dawo ta duniya, inda su ka dawo da bangarorin harsunan duniya kamar Faransanci da Japananci da kuma yaren Portugal.
Kazalika ya ce Jami’ar ta mayar da koyan daya daga cikin kowanne yare wajibi ga ko wane dalibi kafin kammala digirinsa a Jami’ar.