Wasu ‘Yan bindiga da su ka kai hari a yankin unguwar Dankali a ƙaramar hukumar Zariyan jihar Kaduna, sun hallaka mutane 4 tare daji wa mutane 4 rauni bisa harbin su da bindiga.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna Mansur Hassan ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma bayyana cewa yayin harin, jami’an su sun samu nasarar tseratar da mutane 5 da aka yi garkuwa da su, kuma sun cafke ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da aikata laifin.

A cikin waɗanda aka tseratar ya bayyana sunansu inda yace akwai Halima Musa, Ruƙayya Salisu, Ummi Sadisu, Yusuf Musa da kuma Aisha Rabiu.

Mansur Hassan ya ƙara da cewa, harin ya faru ne ranar Juma’a inda bayan sun samu kiran waya, sashen ƴan sanda na ƙaramar hukumar Zariya suka bazama zuwa wurin, inda suka tarar da mutane 6 cikin yanayin matsanancin ciwuka.

Ya kuma ƙara da cewa a take suka garzaya da waɗanda suka samu ciwuka zuwa asibitin Muslim da ke cikin garin Zariya, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar 4 daga cikinsu, yayin da ragowar kuma aka shiga aikin ceto rayuwar su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: