Wasu matasa biyar sun rasu a sanadiyyar hadarin mota da ya auku a hanyar zuwa daurin aure a makon da ya gabata.

Manema labarai sun ruwaito cewa hadarin da ya yi matukar muni kuma ya auku ne a hanyar birnin Katsina zuwa garin Kano a ranar Lahadi.

Motar ta yi hadari ne a garin Tsanyawa, sai da ta tsallaka dayan gefen titi, sannan ta bugi wata mota mai dauke da kaya.

Majiyar ta ce da ‘yan sanda ne su ka ciro su daga motar, kuma an yi gaggawar kai su asibiti inda aka tabbatar da dukkaninsu sun rasu.
Matasan abokan juna ne da tun a makarantar sakandare, sun yi karatu a makarantar kimiyyar kwana ta Ulul Albab da ke garin Katsina.
Bayan shekaru shida su na tare, a shekarar 2011 su ka kammala karatun sakandare, a halin yanzu su na aiki a wurare daban-daban.
Wani wanda ya yi karatu tare da mamatan, ya ce abin ya faru ne da su kan hanyar zuwa daurin auren abokinsu na makaranta.