Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta dawo da shirin ‘Tradermoni’ na tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari a watan Nuwamba.

 

Wannan karo masu cin gajiyar shirin za su samu Naira dubu 50 don taimakawa harkokin kasuwancinsu madadin dubu 10 da ake bayarwa a.

Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu ita ta bayyana haka a gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi 8 ga watan Oktoba a Abuja.

 

Sanarwar ta ce a yanzu karon farko, ta ce a watan Nuwamba za su zabi babbar kasuwa a mazabu uku da su ke da su a ko wace jihar don ba da tallafin ga ‘yan kasuwa.

Edu ta ce wadanda za su ci gajiyar shirin za a zabe su ne ba tare da bambanci na jam’iyya ko alfarma ba a cikin al’umma.

 

Ta ce bayan an zabi masu cin gajiyar, za a bude musu asusun banki wanda za su samu kudadensu ta ciki daga Babban Bankin Najeriya, CBN.

Har ila yau, Edu ta ce wadannan kudade da za a bayar babu kudin ruwa a ciki kuma duk wadanda su ka biya za su samu damar karɓar karin wasu kudaden a gaba.

 

Ta tabbatar da cewa wannan shiri ba shi da alaka da siyasa kuma an kirkiri shirin ne don tallafawa mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: