Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da sace ɗalibai guda huɗu, a jami’ar jihar Nasarawa da ke garin Keffi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Ramhan Nansel ya ce, an sace ɗaliban ne cikin daren jiya bayan ƴan ta’addar sun farmaki yankin Unguwan Ka’are.

Ya kuma shaida cewa, Kwamishinan ƴan sandan jihar Maiyaki Baba, ya bayar da umarnin farmakar masu laifin dan kuɓutar da ɗaliban ba tare da ko ƙwarzane ba.

Nansel ya ce “mun samu labarin afkuwar harin da misalin ƙarfe 12:55 na dare, bayan mun karɓi kiran gaggawa akan cewa wasu mahara sun mamayi wani gida a yankin Unguwan Ka’are.

“Tuni jami’an ƴan sanda bisa haɗin guiwa da sauran jami’an tsaro muka dirarwa yankin, amman bamu samu nasarar cin musu ba.”

Waɗanda lamarin ya faru da su an bayyana sunansu kamar haka, Rahila Hanya, Josephine Gershon, Rosemary Samuel da Goodness Samuel. Dukkansu ƴan aji ɗaya a jami’ar.

Lokacin da aka tuntuɓi jami’an yaɗa labarai na jami’ar Abraham Ekpo, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: