Hukumar shirya jarabawa ta ƙasa NECO ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta 2023 wato SSCE.

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa, shugaban hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne ya sanar da fitar da sakamakon jarabawar a yau Talata, 10 ga watan Oktoban 2023.
Wushishi ya ce kaso 61.60 cikin 100 na ɗaliban da suka zauna jarabawar sun samu kiredit biyar zuwa sama waɗanda suka haɗa da Ingilishi da Lissafi.

Ya ƙara da cewa, an gano makarantu 93 waɗanda gaba ɗaya satar amsa suka yi, yayin da aka bayar da shawarar dakatar da masu sa ido 52 saboda rashin kulawa, ba da taimako, da bada tallafi a lokacin jarabawar.

Wushishi ya ce za a gayyaci makarantun da suka yi satar amsar zuwa hukumar domin tattaunawa, bayan haka za a yi musu hukuncin da ya dace.
Ya ce ɗalibai 1,196,985 da suka haɗa da maza 616,398 da mata 580,587 ne suka zana jarrabawar, ya kuma ce ɗalibai 1,543 masu bukata ta musamman ne suka zana jarabawar.