Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kashe kudi har Naira Biliyan 217, domin aikin gaggawa na gyaran tituna 260 a jihohin Najeriya 36 har da birnin tarayya Abuja.

Ministan ayyuka David Umahi ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis yayin da yake zantawa da ƴan jaridun fadar shugaban Ƙasa, bayan ganawarsa da shugaba Tinubu a Abuja.

Umahi ya kuma bayyana cewa shugaban ya amince da ƙarin ayyukan gina tituna, dan nuna himmarsa ga haɓaka tituna a faɗin ƙasar.

Ya bayyana cewa shugaban ya amince da da sake shinfiɗar babbar gadar ƙasa ta uku, gina titin hanyar zuwa tashar jirgin ruwa ta Lekki da ke Legas da kuma sake gina wasu karyayyun gadoji guda biyu a Inugu.

Sannan ya kuma amince da sake gina wuri biyu a hanyar Imo zuwa Uwerri, da kuma ɗaga likkafar titunan hanyar Abuja, Keffi, Akwanga zuwa Lafiya, da kuma mayar da Titin yanken hanyar Lafiya zuwa Hannu biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: