Hukumomin jami’ar kimiyyah da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Kano, ta sanar da cewa bata ɗiban sabbin ma’aikata.

Hakan ya saɓa da rahotannin da su ke yawo a kafofin sada zumunta na zamani, cewa tana gaf da fara tantance mutane dan ɗiban ma’aikata.

Mataimakin magatakarda na makarantar akan sadarwa Malam Abdullahi Datti, shi ne ya sanar da hakan cikin wani jawabi a yau Litinin.

Datti ya ce “Hukumar jami’ar tana sanar da cewa, labarin da ake yaɗawa ba gaskiya bane kuma bashi da tushe ballantana makama, don haka jama’a su yi watsi da shi.”

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, Abdullahi ya yi kira ga al’umma, da su guji yaɗa labarin ƙarya dan kaucewa ruɗar da mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: