Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi umarnin rushe duk wasu gidajen karuwai, maɓoyar ɓata gari da sauran ayyukan laifuka cikin awanni 72.

Zulum ya bayar da wannan umarnin ne biyo bayan wani wuri da ya ziyarta a unguwar Bayan, mazauna ce da ke kusa da gidajen ma’aikatan titin Layin dogo a Maiduguri.

Yankin yana tara tsageru, ayyukan laifi da kuma ƙananan ayyukan baɗala da ake bayar da kuɗi.

Gwamnan ya nuna damuwarsa akan ƙaruwar ayyukan laifi wanda ke da alaƙa da gidajen karuwai da maɓoyar ɓata garin. Kamar karuwanci, sayar da miyagun ƙwayoyi da sauran ayyukan laifi.

Ya bayyana cewa ayyukan laifin ba iya barazana ce ga tsaro kawai ba, har da dawwamar da miyagun ɗabi’u cikin al’umma, wanda su ke lalata zaman lafiyar al’umma da taɓa mutuncin masu aikatawa.

Kuma bayan an bayar da awanni 72 don rushe wuraren baɗalar, Zulum ya bai wa masu aikata munanan ɗabi’un awanni 12 kacal da su bar wajen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: