Majalisar dokokin Najeriya ta tantance tare da amincewa da nadin Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya.

 

Nadin sabon shugaban ya biyo bayan dakatar da Abdurrashid Bawa wanda ake tuhumarsa kan wansu zarge zarge.

 

An tantance Olu Olokoyede yau Laraba a zaman majalisar.

 

Sabon shugaban hukumar ta EFCC a cikin jawabinsa na majalisar ya buga misali da cewar In da za su yi bincike a kan shugaban majalisar dattawa.

 

Sai dai shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya ce kada sabon shugaban ya yi misali da shi wajen bincike.

 

Sai dai ana zargin shugaban majalisar da badakalar kudi naira biliyan 108.1.

 

Shugaba Bola Tinubu ne ya amince da nada Olu Olokoyede a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa da aka fi sani da EFCC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: