Wata gobara da ta faru a cikin wanii jirgin ruwa ta yi sanadiyyar rasa rayuwar yara biyu tare da jikata wasu mutane biyu a jihar Neja.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Salihu Garba ne ya tabbatar da haa yau Asabar yayin da yake ganawa da jaridar Punch.
Ya ce sun samu labarin tashin gobarar wadda ta faru a karamar hukumar Katcha a jihar a yammacin ranar Juma’a.

Ya ce jirgin na dauke da mutane 145 kuma gobarar ta faru ne sakamakon jarkokin man fetur da jirgin ya dakko.

Kuma mutanen na kan hanyarsu ta kmawa garin Danbo a jihar Kogi bayan cin kasuwa da su ka yi a karamar hukumar Katcha ta jihar Neja a ranar Juma’a.
Sannan sun samu gawar mutum guda yayin da ae ci gaba da neman daya gawar zuwa yanzu.