Rundar yan sanda a jihar Gombe ta tabbatar da mutuwar wata mata mai suna Aishatu Abdulahi da ake zargi masu fashin waya ne su ka hallakata.

An gano gawar matar mai shekaru 58 a duniya a gidanta da ke unguwar Jeka Da Fari a jihar Gombe.

A wwata sanarwa da mai magana da yawun yan sandan jihar Mahid Mu’az ya fitar, ya ce an hallaka matar ne sannan aka yi awon gaba da wayarta.

Sai dai bayan samun labarin, kwamishinan yan sandan jihar ya bayar da umarnin gaggawa dmin ganin an binciko tare da kamo wadanda su ka aikata llaifin.

Al’amarin ya faru a daren ranar Juma’a kuma sun sameta a cikin jini, bayan samunta su ka yi gagagwar kaita asibiti kuma a nan ne aka tabbatar ta rasu.

Yan sanda a jihar sun bayar da tabbacin za su yi bincike tare da tabbatar da kama mutanen da ake zargi.

Sannan sun bukaci mutane su kwantar da hankalinsu, tare da tabbatar da ci gaba da bin doka da oda a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: