Connect with us

Labaran ƙetare

Isra’ila Tana Shirin Korar Falasɗinawa Ne Daga Ƙasarsu – Ambasadan Falasɗin

Published

on

Ambasadan ƙasar Falasɗinu a Najeriya Abdallah Shawesh ya yi zargin cewa, ƙasar Isra’ila ta na shirin korar Falasɗinawa zuwa ƙasar Masar.

Ya yi wannan zargin yayin da yake jawabi a wani taro a birnin tarayya Abuja makon da ya gabata, kwanaki biyo bayan harin da Isra’ila ta kai asibitin Ahli Arab da ke Gaza wanda yayi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan Falalɗinawa.

Shugabannin ƙasashe duniya dai sun yi Allah wadai da harin tare da gudanar da mamakon zanga-zanga a ƙasashen Larabawa da Musulmai.

Shawesh ya ce Isra’ila ta kitsa harin ne a da nufin korar Falasɗinawa daga yankin na Gaza.

Inda ya bayyana cewa bayan harin ya afku, mai magana da yawun Fara-ministan Isra’ila Hanania Naftali ya yi rubutu a shafin sadarwarsa na X wanda ya nuna cewa Isra’ila ta tarwatsa Asibitin na Gaza, kafin daga bisani kuma ya goge rubutun.

Abdallah ya kuma nuna tsananin damuwa bisa yadda shugabannin yammacin duniya su ke goyon bayan Isra’ila, dan tabbatar da shirinta na korar Falasɗinawa daga ƙasarsu.

Ya kuma ce lokaci da ya kamata hukumomin duniyar su tsaya waje guda, don tabbatar da wanzuwar doka bisa tsari.

A Ƙarshe yace ƙasarsa a shirye take don zama da Isra’ila a shawo kan matsalar, domin ƙasarsa a koyaushe tana girmama tattaunawa a abubuwan da suke faruwa tsakanin kasashen biyu.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran ƙetare

Ya Kamata A Dinga Jefe Ƴan Luwaɗi Da Maɗigo – Shugaban Ƙasar Burundi

Published

on

Shugaban kasar Burundi, Evariste Ndayishimiye ya bayyana matakin da ya kamata a rinka dauka kan masu neman maza waɗanda aka fi sani da ‘yan luwadi.

Evariste ya ce kamata ya yi a rinka jefe su da su da masu auren jinsi inda ya ce hakan ba wani laifi ba ne.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jaridu a ranar Juma’a 29 ga watan Disamba.

Ya ce kasarsa ba ta bukatar duk wani taimako daga kasashen Yamma a kokarin kakaba musu sharadin luwadi da madigo.

Har ila yau, shugaban ya ja aya a cikin littafin Inijla inda ya ce Ubagiji ya haramta neman jinsi kwata-kwata.

Ndayashimiye ya kara da cewa kasarsa bata bukatar fara tattauna magana kan ‘yan luwadi da masu auren jinsi.

Ya ce luwadi da madigo hanya ce a bayyane tsakanin hanyar gaskiya ta ubangiji da kuma hanyar bata ta shaidan.

Burundi na daga cikin kasashen Afirka da suka haramta luwadi wanda hakan ya sa aka sanya hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.

Continue Reading

Labaran ƙetare

Shugaban Ƙasar Madagaska Andry Rajoelina Ya Lashe Zaɓe A Karo Na Biyu

Published

on

Shugaban ƙasar Madagaska Andry Rajoelina ya sake lashe zaɓe karo na biyu, duk da kuwa ƙauracewa yin zaɓen da ƴan tsagin masu hamayya suka yi a yankin kudu maso Gabashin ƙasar ta tsuburin Afirka.

Andry ya samu kaso 58.95 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, wanda hukumar zaben ƙasar ta sanar a yau Asabar.

Ƴan takarkarun tsagin hamayya Siteny Randrianasoloniaiko da Marc Ravalomanana sun samu kashi 14.4 da kuma kashi 12. 1 kowannensu.

Ƴan takarkarun tsagin hamayya su goma sun yi kira ga magoya bayansu da su ƙauracewa yin zaɓen, duk da kuwa an sanya sunayensu a jikin takardar ƙuri’ar zaben da aka riga aka buga.

Hukumar zaɓen ta ce kaso 46 cikin 100 sun fito kaɗa ƙuri’a, amman ba a ga fuskar ko ɗaya daga cikin ƴan takarkarun hamayya 12 a wajen sanar da sakamakon zaɓen ba ranar da safiyar yau Asabar.

Ƴan siyasar tsagin hamayyar sun zargi shugaba Rajoelina da ƙoƙarin cigaba da mulki ta hanyar da bata dace ba, sun zargi shugaban da bai’wa kotuna da jami’an hukumar zaben cin hanci.

Continue Reading

Labaran ƙetare

Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Tsawon Awanni Huɗu Kullum A Arewacin Gaza

Published

on

Ƙasar Isra’ila ta amince a tsagaita wuta na awanni huɗu a kullum a arewacin Gaza, don a bai’wa fararen hula damar ficewa daga yankin.

Fadar gwamnatin Amurka ce ta sanar da hakan a yau Alhamis, duk da cewa shugaban ƙasar Joe Biden ya ce babu cikakkiyar tsagaita wuta.

Biden ya yabawa Fara-ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bisa ɗan dogon hutu a faɗan, bayan tsawon wata daya da aka ɗauka ana fafata rikicin.

Sojojin Hamas da Isra’ila yanzu kowanne yana maɓoyarsa, kusa da inda ake gwabza faɗan a birnin Gaza, a yankin arewacin Zirin Gaza.

Mai magana da yawun sashin tsaron ƙasar  John Kirby ya sanar da manema labarai cewa, Isra’ila za ta fara Ƙaddamar da Dakatar da faɗan na awanni huɗu a kullum a yankin na Arewacin na Gaza.

“Isra’ilawa sun sanar da mu cewa, ba za a samu aikin sojin su a yankin ba na tsawon lokutan da aka ɗauka, kuma hakan zai fara daga yau.”

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: