Hadin gwiwar Jami’an tsaron soji ‘yan sanda DSS da sauran jami’an tsaro sun samu nasarar kuɓutar da mutane uku daga hannun ‘yan bindiga a Jihar Kebbi a ranar Lahadi.



Rahotanni sun bayyana cewa hadin gwiwar jami’an tsaron sun ceto mutanen ne bayan yin garkuwa da su a dajin Kanzanna da ke ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar.
A harin da jami’an suka kai’wa ‘yan ta’addan sun hallaka dan bindiga daya, da dama kuma suka tsere dauke da raunuka.
Jami’an sun samu nasarar ne ta cikin wani sumame da da su ka kai maboyar ‘yan bindigar da ke Jihar ta Kebbi.
Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartarwa na Jihar ta Kebbi, Abdulrahman Usman, ya ce gwamnan Jihar Nasiru Idris ya bayar da umarnin tura karin jami’an tsaro Jihar.
Usman ya ce gwamnan ya bayar da umarnin kara aikewa da karin jami’an tsaro zuwa kananan hukumomin da ‘yan bindiga suka mamaye domin tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar.
Sannan ya kuma bayar da umarnin samar da wadattun kayan tallafin kayan aiki ga jami’an tsaro domin kara inganta tsaron ayyukan mutanen Jihar.