Gwamnatin jihar Ogun ta sha alwashin zakulo mutanen da ake zargi da yi wa wasu dalibai mata fyade a jihar.

 

A ranar Talata ne aka yi wa daliban jami’ar Tai Solarin University of Education fyade.

 

Ana zargi yan fashin sun yi wa mata hudu na jami’ar fyade wandanda su ka yi wa jami’ar kawanya.

 

Mataimakiyar gwamnan jihar ta tabbatar da cewar za su tabbata an kamo mutanen da su ka aikata fyaden.

 

A wata sanarwa da aka aikewa da manema labarai a yau bayan da geamnatin ta bayar da kudin da za a duba kafiyar daluban.

 

Ta ce gwamnatin na sane da bayan da shugaban karamar hukumar ya sanar da su.

 

Ta ce gwamna Dapo Abiodun ya bayar da umarni ga jami’an tsaro domin kama mutanen.

 

Gwamnatin ta yi Allah wadai da laifin fyaden da aka yi wa daluban.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: