An sake hallaka mutane biyu a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

 

Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun kashe mutane biyu yayin da su ka jikkata mutane uku a wani sabon hari da su ka kai kauyen Bagoma Dam a jihar Kaduna.

 

Garin Bagoma Dam hanya ce da ke kaiwa zuwa jihar Neja.

 

Wani shugaban tsaro a karamar hukumar Birnin Gwari Ibrahim Abubakar ya bayyana cewa, lamarin ya faru a yammacin ranar Talata a wani gidan mai a garin.

 

Wandanda lamarin ya rutsa da su akwai yan kumgiyar tsaro ta sa kai da kuma wani dan gudun hijira da ya taso daga yankin Dagara.

 

Haka kuma shugaban tsaro a yankin ya shaida cewar an jikkata mutane uku da mummunan rauni, sannan an yi garkuwa da wasu da dama.

 

Al’amarin garkuwa da mutane ya zama tamkar ruwan dare musamman a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: