Rundunar ƴan sanda a jihar Bauchi ta kama wani Adamu Yakubu bisa zargin hallaka ƙaninsa domin karɓe baburinsa.

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar Ahmed Wakili ne ya bayyana haka yau Juma’a, y ace wanda ake zargin ya kashe ƙanin nasa ne a ta hanyar amfani da wuƙa.
A sanarwar da kakakin ya fiyar yace wanda ake zargin ya bayyana musu cewar ya fara satar babur ne tun a shekarar 2020.

Wanda ake zargin y aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Oktoba bayan da wani Usman Mohammad ya kaiwa ƴan sanda rahoto.

Sannan yay i amfani da wuka mai kaifi ya hallaka ƙanin nasa da nufin karɓe masa babur.
A binciken da su key i sun gano cewa, wan da ake zargin ya taɓa satar wani babur a shekarar 2020 sannan ya siyar da shi a kan kuɗi naira 70,000.
A wani cigaban kuma ƴan sanda a jihar sun kama wasu mutane biyu da ake zargi masu garkuwa ne a ƙaramar hukumar Toro a jihar.