Jami’an sojin Najeriya sun samu nasarar kuɓutar da mutane biyu daga hannun masu garkuwa a ranar Alhamis.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun sojin Najeriya Onyema Nwachukwu ya fitar a yau Juma’a.
Kakakin yace mutane biyun da aka yi garkuwa da su masu yi wa ƙasa hidima an tafi da su ne a garin Yargoje da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar.

Bayan samun bayanai a kai, su ka haɗa kai da sauran jami’an tsaro tare da tabbatar da cetosu cikin ƙoshin lafiya.

Sanarwar ta ce zuwa yanzu masu yi wa ƙasa hidimar na ƙarƙashin kulawar jami’an ƴan sanda na ƙaramar hukumar ƙanƙara domin kula da lafiyarsu.
Janar Onyema ya yabaa al’umma a kan hadin kai da su ke bayarwa, tare da buƙatar ci gaba da haka a nan gaba domin daƙile muggan ayyuka.