Gwamnan jihar Zamfara ya bukaci hukumar rage radadi a Najeriya da ta fadada aikinta har ga mutanen da su ka tagayyara a sanadin hare-haren yan bindiga.

Gwamnan na wannan jawabi ne yayin da gwamnan ya ziyarci mahuntan da ke jihar, wanda ya bukaci su fadada ayyukansu don talkafawa mutanem da harin yan bindiga ya shafa.


A yayin ziyarar gwamnan ya ayyana jihar Zamfara a matsayin wadda ke fama da matsakar tsari kuma ya ce hakan ya sa su ke bukatar agaji.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idirs ya sanyawa hannu, ya ce gwamnan ya bukaci a fadada aikin gina gidaje da ake yi a jihar ga mutanem da za a tallafawa, ta yadda zai tiski mutanen da garin yan bindiga ya shafa.
Sannan ya ce a shirye su ke domin hada hannu ko yin aikin hadin gwiwa ta yadda za a ragewa sama da mutane 2,000 radadin wahala da su ke ciki a jihar.
Yayin da yake mayar da jawabi, kwamishinam jin kai na kasa tare da tallafawa masu gudun hijira Tijjani Aliyu Ahmed, ya tabbatarwa da gwamnan cewar za su cigaba da taimkawa jihar Zamfara.
Sannan ya yabawa gwamnan a bisa ziyarar da ya kai masa tun bayan zamansa ahugaba a hukumar.
Haka kuma ya sha alwashin taimakawa da fuska daban daban musamman kayan agaji na gaggawa domin rage radadi ga mutanen da ke fama da hali na kunci a jihar.