Wasu yan bangar siyasa sun fara kai farmaki ne a yankin Agorogbene mai lambar akwatin zabe, 6, 7 da 8 a gunduma ta 11, da ke Kudancin Ijaw, inda suka lalata kayayyakin zabe.

Yan bangar siyasar, sun fara harbe-harbe da bindiga, a lokacin da wasu daga cikin masu zaben suka yi yunkurin dakatar da su daga satar kayan zaben.
Har ila yau, sun mamaye cibiyar yi wa mutane rijista, tare da kwashe kayayyakin zabe na rumfunan zabe biyar daga cikin bakwai da aka ajiye a cibiyar.

A unguwar Ogiadiama, rumfar zabe ta 14 a karamar hukumar Ijaw ta kudu, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gundumar, amma jami’an tsaro sun fatattake su.

Har ila yau an yi garkuwa da jami’in sa ido ga jami’an zabe (SPO) na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da aka tura gundumar zabe mai lamba 06 a garin Ossioma da ke karamar hukumar Sagbama, jihar Bayelsa.