Jami’ar Bayero ta Kano BUK ta sanar da dakatar da jarabawar zangon farko na shekarar 2022/2023 sakamakon yajin aikin da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka fara.

Sanarwar da mai rikon mukamin magatakardan jami’ar, Amina Abdullahi Umar, ta fitar ta bayyana cewa hakan ya zama dole ne bayan yajin aikin da kungiyoyin kwadagon suka tsunduma.


Sanarwar ta bukaci daliban jami’ar da su kwantar da hankalinsu tare da jiran umarni na gaba.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta umarci mambobinta da su marawa kungiyoyin kwadago baya wajen shiga yajin aikin da kungiyoyin su ka fara.
Yajin aikin na kungiyoyin kwadagon na zuwa ne a matsayin martani ga cin zarafin da ake zargin ’yan sandan Najeriya da gwamnatin jihar Imo suka yi wa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, sai dai wadanda ake zargin sun musanta hakan.
Tuni dai ayyuka suka samu cikas a fadin Najeriya a sakamakon yajin aikin da aka fara ranar Talata.