Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu, zai bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya domin kai ziyara kasar Guinea Bissau a gobe Alhamis, domin taya murnar bikin cika shekaru hamsin da samun yancin kai a kasar.

 

Mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Nglale, ne ya bayyana haka yau Laraba a birnin Jiddah da ke kasar Saudiya inda shugaban kasar ke gudanar da ibadar Umara.

 

Ya ce shugaban kasar zai sauka a Bissau gobe Alhamis, domin taya murnar shagalin bikin kamar yadda ya samu gayyata daga shugaban kasar ta Guinea Bissau, Umaro Embalo

 

Kasar Guinea Bissau dai na bikin cika shekaru hamsin ne da samun yancin kai, kuma bikin na wannan shekarar ya zagayo ne tun ranar 24 ga watan September, amma sai dai gwamnatin kasar ta mayar da bukukuwan na wannan shekarar zuwa 16 ga watan Nuwamba.

 

Ana sa ran shugaban kasar zai dawo Najeriya a ranar Juma’a.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: