Rundunar ƴan sanda a jihar Kaduna, ta ce sun yi nasarar kubutar da mutane uku da aka yi garkuwa da su a kauyen kidandan da ke karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.

 

Mai magana da yawun rundunar, ASP Mansur Hassan, ne ya fada wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN hakan yau Laraba a Kaduna, inda ya ce rundunar ta kubutar da mutanen ne a ranar Litinin din da ta gabata.

 

Ya ce nasarar kubutar da mutanen ta samu ne sanadiyar jajircewar da jami’an yan sanda tare da gudunmawar al’umma wajen dakile ayyukan bata-gari.

 

Ya kara da cewa maharan sun yi garkuwa da mutanen ne tun ranar 3 ga watan Oktoba na wannan shekarar da mu ke ciki, akan hanyar hanyar Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja.

 

Tuni dai mutanen da aka kubutar din aka damka su zuwa ga iyalansu.

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: