Wata gobara da ta faru a sansanin ƴan gudun hijira ta yi sanadiyyar ƙone gidaje 1,113 sannan yara biyu sun rasu.

 

Gobarar da ta faru a sansanin ƴan gudun hijira a jihar Borno kuma ta shafe fiye da awa guda ta na ci.

 

Babban darakta a hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Dakta Barkindo Muhammad ya tabbatar da haka yayin da ya ziyarci sansanin da ke Muna Alamdari a Maiduguri babban birnin jihar.

 

Ya ce wutar ta fara ne tun ƙarfe shida na asubahi kuma ta shafe fiye da awa guda kafin masu hukumar kashe gobara ta samu damar kashe gobarar.

 

Sannan jami’ai da dama sun bayar da gudunmawar su wajen kashe gobarar.

 

Ya ce zuwa yanzu sun kai buhun shinkafa 500 da wasu kayan amfani domin bayar da agajin gaggawa.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: