Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ta ce jami’anta sun bi diddigi tare da gano wasu shanu guda uku da aka sace, a gidan Muktari Ibrahim da ke Sabuwar Unguwa, karamar hukumar Kiyawa.

DSP Lawan Shiisu Adam, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, ya shaidawa manema labarai cewa, sun gano Ibrahim mai shekaru 23, biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu.
Adam ya ce, a ranar 13 ga watan Nuwamba, da misalin karfe 8 na safe, wani Umar Musa da Idris Ismail daga kauyen Malamawa, karamar hukumar Kiyawa, suka kai rahoton sace shanun.

A cewar sa, mutanen sun bayyana wa hukumar cewa barayi da misalin karfe 3 na safe sun sace shanu uku a gidajensu wanda kudinsu ya kai naira miliyan 1,150,000.

Manema labarai sun ruwaito cewa, kakakin rundunar ya ce, Ibrahim ya bayyana masu cewa ya karbi shanun da aka sato daga hannun wani mutum mai suna Yusuf, tare da wasu mutane.
Ya kara da cewa, rundunar ta kwato shanun tare da mayar da su ga mamallakan su, yana mai jaddada cewa hukumar ‘yan sanda na ci gaba da tsaurara bincike don cafke wadanda suka tsere daga cikin barayin shanun.
Ko a shekarar 2021, sai da hukumar tsaro ta NSCDC ta damke wani wanda ake zargin barawon shanu ne da wani mai safarar miyagun kwayoyi a jihar Katsina.