Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ya ce akwai tabbacin za su sake nakasa NNPP a kotun koli.
Ganduje ya bayyana haka ne yayin da ya ke martani kan hukuncin kotun da aka yanke a yau Juma’a 17 ga watan Nuwamba.
Ya ce ya ji dadin wannan hukunci na kotu kuma ya tabbata Abba Kabir zai sake daukaka kara inda ya ce za su sake karbar hukunci a kotun koli.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana haka ne ga manema labarai a Abuja a yau Juma’a 17 ga watan Nuwamba.
Wannan martani na Ganduje na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta sake tabbatar da kwace kujerar Abba Kabir na jam’iyyar NNPP a matsayin gwamna.
Kotun ta kuma sake tabbtar da nasarar Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.