Gamayyar wasu kungiyoyi guda 11 dake jihar kano sun ce Sun bi diddigi tare da tuntubar waɗanda shirin AGILE ya shafa ya shafe a jihar Kano don gano zargi da wasu ke yi na muzanta shirin, kuma sun gano wadancan bayanai ba su da tushe ballantana makama.

Ƙungoyin da su ka haɗa da

-Network For Youth Enlightenment And Development N-YED,

-Association of Nigerian Women and Youths for Peace Advocates
(ANWOPA) Kano chapter, Youth
-Mobilization by Media,

-Fighting Against –
•Women and Children Violation, Kano
Youth Progressive Concern,

-Arewa Peace Ambassadors,

-NACCRAN Kano State,

-Arewa Youth Innovative of Nigeria.

Kano Progressive Mindset Forum.

Kano State Network for youth Initiative.
Arewa Youths Political Gladiators (AYPG),

-Kainuwa Youth Progressive Community Development.

-African Emancipation Movement (Kano Chapter),

Arewa Students Forum,

-Daliban Nigeria Reshan jahar Kano

-KASYADREC ( DRUGS ORG.)

Gamayyar kungiyoyin sun ce sun bibiyi wadanda abin ya shafa musamman gwamnati da jami’an shirin, da wasu daga cikin iyayen yaran sama da 800,000 dake makarantun gwamnati a jihar Kano, da su kansu daliban, da malaman da ke ba da horon, da sauran masu ruwa da tsaki.

Haka kuma sun bibiyi ita kanta manhajar da ake horar da yaran, tare da sauran manhajojin sauran darussan sakandire, ba su sami wani dalili da za a ce shirin ya saɓawa Addini, ko al’adu da kuma zamantakewa ba, amma ba su samuba.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren gamayyar kungiyoyin Amb. Nura Abdullahi Saraki ya sanyawa hannu kuma aka ranar Juma’a.

“Don haka wannan batu ƙage ne mara tushe da muka kasa gane abinda masu yada shi ke burin cimma, sabanin cigaban al’ummar Jihar Kano baki daya” a cewar sanarwar.

A zurfafa bincikensu, sun tabbatar da cewa gwamnatin Kano ta fara gudanar da shirin AGILE tun shekarar 2021, tare da jihohin Bomo, Katsina, Kaduna, Kebbi, Plateau da Ekiti.

“Kuma saboda amfanin shirin a yanzu haka wasu karin jihohi sun sami nasarar shiga.

Kamar Jigawa, Zamfara, Bauchi, Gombe, Yohe, Kogi, Niger, Kwara da sauransu.

Rawar da Bankin Duniya ke takawa kawai ita ce ya ba da lamunin kudaden gudanarwa, wanda kurna za a biya cikin wasu shekaru nan gaba”.

” Mun bincika kuma mun tabbatar shirin AGILE ba shi da wata alaka ta kusa ko ta nesa da Yahudawa, ba kamar yadda ake zuzuta hakan, a Fili ko a boye.

Kuma dukkan al’umma suna ganin irin alfanun da wannan shiri ya kawo a
makarantun sakandire na duk fadin Jihar Kano”. Inji gamayyar kungiyoyin

Kungiyar ta yi kira ga dukkan jama’a da su bibiyi makarantun yankunansu, iyaye kuma su tuntubi ‘ya’yayansu, domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Kuma sun ce kofar jami’an wannan shiri, da ta mahukunta a bude take ko da yaushe, ga masu neman karin bayani, ko shawara, ko tattaunawa game da dukkan tsare-tsaren wannan shiri, a ofishinsu da ke hawa na uku, Gidan Murtala, Kofar Nassarawa, cikin Birnin Kano.

“Muna shawartar al’umma da mu guji yada jita -jita ba tare da bincike a kan ingancin labarun yanar gizo ba, musamman game da muhimmin kokari da Ma’aikatar Ilimi ke yi wajen inganta rayuwar al’umma domin ci gaban Jihar Kano baki daya”

Leave a Reply

%d bloggers like this: