Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta mika shaidar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo da mataimakinsa.

Hukumar zaben ta mika shaidar ne a hedikwatarta da ke Lokoja a yau Juma’a 17 ga watan Nuwamba.
A jihar Zamfara kuwa kotun daukaka kara ta rusa zaben kananan hukumomi uku inda ta ba da umarnin sake zabe a wadansu wurare.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Bukuyun da Maradun da kuma karamar hukumar Birnin-Magaji.

Yayin martaninshi, Gwamna Lawal ya roki mutanen jihar da su kwantar da hankalinsu kan wannan hukunci.