Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ya ce za su sake ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli ta Najeriya domin neman nasara a kan zaɓen gwamnan.

Injiniya Abba Kabir ya bayyana haka ne a wani faifen bidiyo da yake jawabi a ranar Juma’a bayan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke.

Gwamnan ya ce ba su ji daɗin yadda aka yanke hukuncin ba, kuma rashin gamsuwa da hukuncin da aka yanke ne zai sanya su sake ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli.

A cikin jawabin ya tabbatar da cewar gwamnatin na aiki da sauran jami’an tsaro domin cigaba da tsare rayuwa da dukiyoyin al’umma.

A don haka ya buƙaci mutane da su ci gaba da harkokinsu ba tare da fargaba ba.

Gwamna Abba ya ce za su cigaba da gudanar da ayyuka kamar yadda su ka fara, sannan za su ɗaukaka ƙarar ne zuwa kotun ƙoli domin ƙwato haƙƙinsu.

A ranar Juma’a ne dai kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta kori ƙarar da gwamna Abba Kabir da jam’iyyar NNPP su ka shigar a gabanta, domin ƙalubalantar hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ta ce Dakta Nasiru Yusif Gawuna ne halastaccen gwamnan Kano.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: