Mazauna kauyuka 13 na kudancin jihar Kebbi wadanda yan bindiga suka kora daga matsugunansu, sun koma muhallansu bayan dawowar zaman lafiya a kauyukan.

Mai magana da yawun gwamnan jihar ta Kebbi, Ahmed Idris, ne ya bayyana haka ranar Litinin a Birnin Kebbi, inda ya ce mazauna kauyukan sun dawo matsugunansu.

Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Sawade, Bakin gulunbi, Mai Fanu, Malekaci, Sakawa, Sabongida, kauran mai zanma, Luga, Angela Kibiya, angela dado, tsirinda, Kasama da kuma kauyen Ma’ako.

Da yake karin bayani kan al’amarin,  shugaban karamar hukumar Danko Wasagu, Aliyu Hussaini Bena, ya tabbatar da cewa al’umma kauyukan sun dawo gidajensu, sannan an sake bude manyan kasuwannin kauyukan domin cigaba da gudanar da al’amura.

Daga nan sai ya godewa gwamnan jihar, Alhaji Nasir Idris,  bisa kyakkyawan yunkurinsa na ganin an kyautatawa al’umma tare da samar musu da ingantaccen tsaro.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: