Kotun ɗaukaka ƙara a jiya Laraba, ta ƙara jaddada hukuncinta wanda ya kori gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf.

Babban magatakardar kotun ta ɗaukaka ƙara Umar Bangari ne ya bayyana hakan, yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja.

An samu dai tangarɗar alƙalumma a takardar Kwafin Hukuncin Shari’ar ta gwamnan Kano, wadda Abba Kabir Yusuf ɗin da jam’iyyarsa ta NNPP suke bayyana cewa hakan ya tabbatar musu da nasara a zaben gwamnan da ya gudana ranar 18 ga watan Maris.

Umar Bangari yace abinda aka gani a takardar Kwafin shari’ar kuskuren ɗab’i ne, wanda hakan baya nufin ko kuma canja hukuncin da kotu ta yi.

Ya kuma ce, za a iya gyara hakan kuma idan ɓangarorin biyu suka buƙaci yin hakan.

Ya kuma ja hankalin manema labarai da su duba kundin littafin dokar kotun ɗaukaka ƙara doka ta huɗu, wacce ta baiwa kotun ɗaukaka ƙara damar gyara duk wani kuskuren ɗab’i da aka samu.

A ƙarshe ya kuma bayyana cewa, hukuncin da kotun ta ayyana yana nan daram saɓanin yadda ake ta raɗe-raɗin Lalacewar sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: