Gwamnan Jihar Katsina Umar Dikko Radda ya amince da biyan naira miliyan 977, don biyan kudin jarrabawar NECO ga daliban Jihar su 48,38.

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da gwamnatin Jihar ta Wallafa a Shafinta na X a ranar Laraba.


Biyan kudin jarabawar ta NECO na zuwa ne kasa da wata guda bayan gwamnan ya biya naira miliyan 364.8 ga daliban da suka rubuta jarrabawar WAEC a Jihar.
Gwamnan ya ce iya dalibai ‘yan asalin Jihar ne da suka rubuta jarrabawar a wannan shekarar za su amfana.
Bayan biyan kudin jarrabawar daliban a jihar sun nuna farin cikinsu a sakamakon haka.
Gaza biyan kudin jarabawa da wasu gwamnonin ke yi hakan na haifarwa da wasu dalibai cikas a harkar karatunnasu wanda hakan ke sanyawa wasu su dakatar da karatun baki daya.