Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya ziyarci shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje a gidansa da ke Abuja.

Ba a san dai Dalili da kuma muhimmin abu da suka tattauna a zayartar tasa ba.
A nasa bangaren tsohon shugaban Jonathan bai ce komai dangane da ziyarar da ya kai wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ba.

Tun kafin dai gudanar da babban zaɓen shekarar 2023, an yi ta alaƙanta Jonathan da yin takarar shugabancin ƙasa a Jami’iyyar ta APC.

Yayin da wasu rukunin al’ummar arewacin Najeriya suka siya masa fom ɗin yin takarar shugabancin ƙasar.
A wancan lokacin dai, shi kansa Jonathan ya gana da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Adamu.
Sai dai tun a wancan lokacin tsohon shugaban ƙasar Jonathan, ya yi burus da ƙin cewa komai dangane da wannan batu lokacin da magoya bayan suka tambaye shi.