Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta soke zaben ‘yan majalisar dokokin Jihar Filato 11 na jam’iyyar PDP, inda ta tabbatar da na jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka samu nasarar.
A wani hukunci da kotun ta yanke karkashin jagorancin mai shari’a Oko Abang a ranar Juma’a, sun bayyana cewa kuri’un da dakatattun ‘yan majalisar suka samu ba su halarta ba a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.
Alkalin ya bayyana cewa jam’iyyar ta PDP ta sabawa dokar sashe na 177 na kundin mulkin Najeriya na shekarar 1999, kuma hakan ya sanya ba ta cancanci tsayar da ‘yan takarar ba.
A hukuncin kotun ta tabbatar da ‘yan takarar na jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka samu nasarar a zaben.
Bayan yanke hukuncin a halin yanzu jam’iyyar APC ce ke da rinjaye a majalisar ta dokokin Jihar ta Filato.