Jami’an sojin Najeriya sun hallaka wasu ‘yan bindiga Hudu a wani sumame da suka kai maboyarsu da ke kauyuka daban-daban na Jihar Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar Operation hadarin daji Kaftin Yahya Ibrahim ne ya bayyana hakan.


Ibrahim ya ce jami’an sun kai harin ne a kauyukan Tazame, Mashema, Maje, Doka, Gandaya, duk da ke karamar hukumar Bungudu ta Jihar.
Kaftin Yahya ya kara da cewa jami’an sun kuma sake kai hari maboyar batagarin, a wani daji da ke kewaye da kauyen Gandaya da ke karamar hukumar ta Bungudu.
Ibrahim ya bayyana cewa da yawa daga cikin ‘yan bindigar sun tsere dauke da raunuka a tare da su, sannan sun lalata sansanonin bata garin.
Kazalika ya ce jami’an sun kuma kwato shanu 57 kayan sojoji da kuma tsabar kudi naira 900,000 da sauran wasu kayayyaki.