Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta gabatar da zanga-zangarta zuwa Abuja saboda abin da ta kira da ana neman soke nasararta a zaben 2023.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa shugabannin NNPP sun ce idan har aka karbe gwamnatin Kano daga hannunsu, za a iya haddasa rikici.

A wani jawabi da Ladipo Johnson ya fitar a ranar Laraba, ya yi gargadi cewa wannan rigima za ta iya shafar har sauran kasashe na Afrika.

Shugaban mai binciken kudi ya karanto jawabin da shugaban jam’iyyar NNPP na rikon kwarya, Abba Kawu Ali ya rubuta a ofishin ECOWAS.

NNPP ta kuma yi tattaki zuwa ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniyya da babban ofishin kungiyar EU ta tarayyar Turai a garin Abuja.

Shugabannin na NNPP sun ce daga hukuncin kotun sauraron karar zabe da na daukaka kara, ta fito cewa ana so a zalunci mutanen Kano.

Jawabin Abba Kawu Ali ya ce mafi yawan al’umma sun zabi Abba Kabir Yusuf na NNPP a watan Maris, amma ana shirye-shirye domin a tsige shi. Sai dai jam’iyyar ta ce bazatayi watsi da takardun CTC da aka fitar ba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: