Mazauna garin Maganda da ke gundumar Magajin Gari ta III a Birnin Gwari, jihar Kaduna, sun tsere daga gidajensu bayan janye sojojin da aka girke a garin.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan garin sun tsere ne don tsoron farmakin ‘yan bindiga wadanda ke addabar garin tsawon shekaru.
Mazauna garin sun bayyana cewa jami’an tsaron da aka girke don kare mutanen garin, sun kwashe kayansu Asabar din da ta gabata, lamarin da ya jefa tsoro a zukatan mutane.

Ismail A. Ahmed, tsohon shugaban kansilan gundumar wanda ya dauke matarsa da yaransa daga garin, ya ce ‘yan bindigar sun far wa garin jim kadan bayan tafiyar sojojin.

Ya ce ‘yan bindigar ba su fuskanci wata matsala ba, inda suka rinka bi gida-gida suna karbar wayoyi da kudade daga hannun mutane.
Ahmed ya kara da cewa ‘yan garin sun hakura sun bar gidajensu, amfanin gonakinsu da wasu kayayyakinsu don tsira da rayukansu.