Gwamnatin jihar Kano za ta fara biyan giratutin ma’aikatan da su ka bar aiki kamar yadda ta dauki alkawari.

Daga ranar Asabar 2 ga watan Disamba 2023, gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf za ta fara biyan kudin kamar yadda aka sanar.
Mai taimakawa gwamnan a kafofin sadarwa na zamani, Abdullahi Ibrahim ya sanar da wannan a yammacin Alhamis a Twitter.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar Kano za ta fara ne da manyan ma’aikatan da su ka yi ritaya daga aiki tsakanin shekarar 2016 da 2019.

Abdullahi Ibrahim ya ce wadanda za a soma biya hakkokinsu su ne wanda kudin sallamarsu bai wuce Naira miliyan uku ba.
Bayan su za a sallami wadanda su ka ajiye aiki daga shekarar 2016 da 2020 wanda kudin giratutinsu bai haura Naira miliyan 2.5 ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki alkawarin zai biya wadannan kudi tun bayan da kotun daukaka kara ta tsige shi daga mulki.
Ma’aikatan da su ka rasu su na bin gwamnatin Kano bashin Naira miliyan uku zuwa kasa, duk suna cikin wadanda za a fara.
Dama can an warewa ‘yan fansho Naira biliyan shida, yanzu ana bukatar duk tsohon ma’aikacin da zai je ya dauki takardun aikin da za a bukata.