Gwamnatin tarayya ta ce sabon mafi karancin albashi da za a fito da shi zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Afrilu 2024 a Najeriya.

Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma, Idris Mohammed ya shaida haka a wata hira da yayi da Punch a birnin tarayya Abuja.

Alhaji Idris Mohammed ya ce tsarin albashin da ke amfani da shi zai daina aiki daga watan Maris, daga nan mafi karancin albashin zai fara.

Ministan ya ce tsarin kashe kudi ya nuna gwamnatin tarayya za ta batar da Naira tiriliyan 24.66tr a kan albashi a shekarun 2024, 2025 da kuma 2026.

A sakamakon cire tallafin man fetur, Bola Tinubu ya amince a rika biyan N35, 000 ga ma’aikatan gwamnati kafin ayi ainihin karin albashi.

Matsin lambar kungiyar kwadago ya jawo gwamnati ta na kokarin yadda za a kara mafi karancin albashi daga N30, 000 da ake biya.

Wani jami’in NLC ya tabbatar da maganar inda gwamnati ta ke fatan gwamnoni da ‘yan kasuwa za su yi wa ma’aikata karin albashin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: