Sakataren watsa labaran APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce ruɗanin da aka samu a kwafin takardar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara (CTC) na zaben gwamnan Kano kuskure ne na ɗan adam.

Morka ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels cikin shirin siyasa a yau.

A baya kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun zaɓe na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

Amma a karshe-ƙarshe daidai shafi na 67 da ke kunshe a cikin kwafin hukunci, an ga kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin kotun zaɓe, wanda ya sauke Abba daga kujerar gwamna.

Morka ya ce ba zai yuwu ka karanta hukuncin guntu-guntu ko ku keɓe wani sashi ku karanta ba, sha’anin shari’a musamman a kotun daukaka ƙara, ana yanke hukunci bisa hujjoji.

Kakakin APC ya ce abinda ya fi muhimmanci shi ne kotun ɗaukaka ƙara ta fito ta yi bayanin kuskuren da aka samu kuma ta gyara.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: