Hukumar Hisbah ta yi nasarar kama wasu mutane da suke cin kasuwar mushen rago da kaji hadi dayin balangunsa.

Kwamandan Hisbah na karamar hukumar Tarauni malam Nasir Adam Mai kaji yace dakarun Hisbah na karamar hukumar Tarauni ne su kayi nasarar kamo mutanen a daidai lokacin da suke yunkurin tafiya da naman mushen domin kaiwa kasuwa.

Kwamandan ya ce abin da takaici yadda mutanen da suke ikirarin su musulmi ne a ce suna ɗaukar mushe a bola su gyara da nufin sayar dashi ga mutane wanda yin hakan ka iya jawo cutuka ga mutane wadanda ba za’a iya gane kansu ba.

Don haka ne ma yayi kira ga al’umma da su himmatu wajen kai mushe da suka samu na daga dabbobinsu gidan kula da namun daji ko kuma su binne shi domin kaucewa budewa bata gari kofar siyar da naman mushe ga al’umma.

Mutanen da aka kama Aminu Abdullahi da Isyaku Musa sun tabbas suna sayar da mushen ne a sabon gari kuma masu amfani da mushen sukan basu kyautar barasa tare da biyansu kudi kuma a gefe guda.

Aminu da isyaku sun ce sun yi nadamar rungumar wannan sana’ar da suka dauki tsawon lokaci suna gudanarwa ba tare da an kamasu ba sai a wannan karon sun kuma yi al’washin daina wannan sana’ar kwata kwata.

Wakiliyarmu Jamila Sulaiman Aliyu ta labarta mana hukumar Hisba ta karamar hukumar Tarauni ta umarci mutanen biyu su binne naman duk da wani balangun mushen da sukayi duk da sun bayyana cewa Suma su na cin balangun da sukayi da mushen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: