Tsohon gwamnan Jihar Neja Dr Mu’azu Babangida Aliyu ya koka game da yadda tsarin zaben kasar ke tafiya a halin yanzu.

Dakta Babangida ya bayyana hakan ne a gurin wani taro da ya halarta a Jihar Kaduna.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa rashin gaskiyar da ake nunawa a lokacin takara hakan na sanyawa mutanen kirki su ware a siyasa.

A cewarsa irin yadda ake tafiya a yanzu, hakan ne zai sanya mutanen kwarai ba za su taba samun takara ba a ƙasar nan.

Mu’azu ya kara da cewa harkar siyasa a kasar ta zama harkar kashewa da neman kudi, a maimakon hidimtawa al’ummar Kasar.
Ya Kara da cewa hakan ne ke sanyawa mutane a kasar ke ganin lamarin ya zamto hanyar samun kudi ga ‘yan takarar.