Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bayyana cewa ya kamata a duba yuwuwar karawa ma’aikatan Kasar albashi a shekarar 2024 mai zuwa.

Shugaban kungiyar na kasa Joe Ajaoro shi ne ya bayyana hakan a gurin wani taron bude wata makaranta a birnin tarayya Abuja.

Kungiyar ta ce ya kamata a yi duba da yadda ake ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa a Kasar, kuma albashin ma’aikatan baya iya wadatar dasu wajen yin bukatunsu na rayuwa.

Ajero ya ce kungiyar za ta yi iya bakin kokarin ta wajen ganin an duba yuwuwar karawa ma’aikatan albashi a fadin Najeriya.

Shugaban ya bayyana cewa tun bayan cire tallafin man fetur da aka yi a kasar ma’aikatan suka shiga cikin tsadar rayuwa da talauci.

Shugaban ya ce ya zama wajibi gwamnatoci a kowanne irin mataki su duba wahalar da al’ummar kasar ke sha tare da samar da makoma.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: