Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wasu mutane biyu da laifin hallaka dan uwansu kan zargin yin maita a Jihar.

Wanda mutanen suka hallaka mai suna Muhammad Sani mai shekaru 35 ‘yan uwan nasa sun hallakashi ta hanyar kulleshi a daki tare da barinshi da yunwa.

Mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan Jihar Shettima Muhammad shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Shettima ya ce ‘yan uwan mutumin sun daure hannayensa da kafafunsa a cikin dakinsa daga bisani suka rufeshi a cikin dakin.

Muhammad ya ce bayan mutuwar Muhammad Sani ‘yan uwan nashi su ka yi gaggawar binneshi.

Ya kara da cewa mutanen sun yi aika-aikar ne tun a ranar 30 ga watan Nuwamba, inda ake ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran wadanda ke da hannun a hallaka mamacin bayan sun tsere.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: