Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da shirin fara bai’wa marasa karfi tallafi a Jihar Kogi domin cire musu radadin cire tallafin man fetur.

Ma’aikatar jin kai da kawar da talauci ta Kasar ce za ta bayar da tallafin.
Ma’aikatar ta kaddamar da shirin ne karkashin jagorancin Betta Edu a ranar Talata inda za a bai’wa mutanen tallafin naira 20,000 kowanne.

Betta Edu ta ce an kafa wata tawaga ta musamman da za ta yi aikin bayar da tallafin domin rage radadin cire tallafin man fetur ga ‘yan kasar.

A yayin bayar da tallafin Edu ta bayyana cewa kudin da aka bai’wa mutanen ba bashi aka ba su ba.
Edu ta ce gwamnatin ta tarayya ta daura aniyar fitar da ‘yan kasar akalla miliyan 50 daga cikin talauci.