Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta sake gina garin Tudun Biri a karamar hukumar Igabi garin da jirgin soji ya hallaka mutane da dama.

Shettima ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai garin a ranar Alhamis.
Kashim ya ce tuni shugaban ya bayar da umarnin sake fasalin garin na Tudun Biri.

Mataimakin shugaban ya kara da cewa gwamnatin za kuma ta gina gidaje da dakunan shan magani, da Asibitin dabbobi a cikin garin.

Kashim Shettima ya bayyana cewa za a fara shirin aiwatar da tsare-tsaren tallafawa al’ummar garin tsarin Fulako wanda za a fito dashi nan bada dadewa ba, tare da sanya musu wuta mai amfani da hasken Rana.
A cewar Shettima za a yi hakan ne domin ragewa mutanen garin radadin halin rasa mutanen garin da suka yi.